By Ishaq Dabai
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya gabatar da kasafin kudi na naira biliyan 294 ga majalisar dokokin jihar Oyo na shekarar 2022 tare da kayayyakin more rayuwa dake samun kaso mafi tsoka.
Makinde, yayin gabatar da kasafin kudin, mai taken, “Kasafin Ci Gaban da Dama,” yace mafi girman abin da aka ware na Naira biliyan 96 wanda ke wakiltar kashi 32.83 bisa dari, zai tafi ne don kayayyakin more rayuwa yayin da Naira biliyan 54, ke wakiltar kashi 18.37 cikin ɗari a fannin ilimi.
Makinde ya kara da cewa gwamnatinsa zata ci gaba da kiyaye al’adarta na kiyaye rabon ilimi sama da matsayin Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO.
A cewar gwamnan, gwamnatinsa ta sami nasarar cimma kashi 60 cikin 100 na kasafin kudin shekarar 2021, inda ya kara da cewa burinsa shine ya samu karin kashi 15 cikin dari na kasafin kudin gaba daya kafin karshen shekarar.
Kazalika Makinde ya bayyana cewa jimillar kasafin kudin sa na kiwon lafiya ya kai Naira biliyan 17, wanda shine kusan kashi 5.9 na jimlar kasafin.