By Ishaq Dabai
An jefa ɗalibai da ma’aikatan jami’ar Ibadan cikin baƙin ciki bayan mutuwar ɗaliban jami’ar biyu a cikin sa’o’i 24.
Daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, Adegoke Adedayo, dalibin shekarar karshe na Sashen Tarihi, an harbe shi ne a lokacin da ake fashi da makami kusa da hanyar Bodija ta jami’ar UI
An bayyana cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi, haka kuma wani dalibin dake karatu a sashen Kimiyyar Halittu na Kwalejin Kimiyya, Ayomide Adeyemo, ya fadi da mota yayin da yake tsallaka hanya kusa da babbar kofar makarantar.
Daraktan yada labarai na jami’ar, Tunji Oladejo, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin na fashi, ya ce ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike.sannan yace, “An kai rahoton lamarin ga ofishin‘ yan sanda na Bodija. Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo na gudanar da bincike cikin hikima kan abin bakin ciki.Gawar marigayin dalibar an kaita Asibitin Kwalejin Jami’ar don yin bincike.”
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar Oyo, Adewale Osifeso, bai amsa tambayoyin wakilan mu ba yayin hada wannan rahoton.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Jami’in hulda da jama’a na hukumar tsaron Najeriya ta farin kaya NSCDC, Oluwole Olusegun, yace hukumar ta samu rahoton cewa wasu da ake zargin ‘yan fashi ne sun harbe wani mutum a kusa da yankin Preboye tsakanin karfe 7 na dare zuwa 8 na dare.
Kazalika Yace, “Da misalin karfe 9 na dare a wannan ranar, wasu gungun‘ yan bindiga sun harbe wani mutum a yankin Civic Center. Inda yace jami’an su suna binciken karar. ”