Wata Kotu dake Rawalpindi ta Ƙasar Pakistan ta yankewa wani Fasto Zafar Bhatti Mai Shekaru 58 hukuncin kisa, sakamakon ɓatanci ga Musulunci.
Bhatti wanda ya kasance yana a gidan yari tun shekarar 2021, an zarge shi da tura saƙon karta kwana na ɓatancin, a cewar Anglican link.
An yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai a ranar 3 ga watan Mayun shekarar 2017 a ƙarƙashin doka ta 295 (a) da na 295 (a) na ƙasar Pakistan cin mutuncin Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama da Mahaifiyar shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zazzabin Cutar Lassa A Jihar Benue Ya Yi Sanadin Ran Likita Guda
Kafin a kama shi a shekarar 2012, Fasto Zafar Bhatti shine Mai mallakin gidauniyar Charity Organization “Jesus World Mission” domin taimakon mabuƙata. Ya samar da coci.
A cewar wani ƙorafi da wani ya shigar da ba’a sanshi ba, ƴan sanda sun kama shi sakamakon zargin ɓatanci ga Musulunci.
Bayan binciken wayar shi, Masu kamfanin layuka sun bayyana cewa lambar da akayi amfani da’ita wajen tura saƙon bashi yayi rajistar ta vay. Wata Musulma mai suna Ghazala Khan ita ke da mallakin lambar da akayi amfani da’ita wajen tura saƙon.
Kotu ta gayyaci matar a watan Afrilu na shekarar 2013, rana ta farko da Zafar Bhatti Amma ya musanta zargin da ake yi mashi.
A ranar 3 ga watan Janairun Sabuwar Shekara, Kotun ta yanke masa hukuncin kisan, duk da ya kasance mazaunin gidan yari daya shafe shekaru a cikin sa.
Ilyas Samuel ya bayyana rashin jindaɗi akan wannan hukunci da kotu ta yanke