Ministan sadarwar Nijeriya, Dk. Isa Ali Ibrahim Pantami ya jinjinawa bangaren bayanai, sadarwa, da kuma fasaha wanda aka fi sani da ICT a turance bisa gudummawar da bangaren ke bayarwa wajen bunkasa tattalin arzikin Nijeriya musamman cikin watanni shida. A rahoton da hukumar kididdiga ta kasa wato NBS ta fitar, ta bayyana cewa; gudummawar da bangaren ICT ke bayarwa a Nijeriya ga bunkasar tattalin arzikin kasar, ya sanya abubuwan da Nijeriya ke samu har ya zarce abin da take samu a bangaren mai da kuma iskar gas cikin watanni shida na shekarar 2019.
Rahoton wanda aka saki a ranar Talata, 2 ga watan Satumban 2019, ya shaida cewa; kasarnan GDP dinta ya karu da kashi 1.94 duk shekara cikin watanni shidan shekarar 2019 musamman idan aka yi la’akari abin da aka samu cikin shekarar 2018.
Ministan sadarwar, Pantami ya tabbatar da cewa; an samu wannan ci gaban ne a bangaren sadarwa saboda irin kyawawan manufofi na shugaban kasa Muhammadu Buhari musamman ma bangaren tabbatar da tsarin ERGP. Ya ce wannan ne ya jawo bangaren da ba na man fetur ba ya zama yana bunkasa tattalin arzikin kasarnan.