A ranar Litinin Shugaban mabiya Darikar Katolika Paparoma Francis ke ziyarar zango na karshe a tsibirin Mauritius daga cikin jerin kasashen Afrika 3, inda ake sa ran ya jinjinawa hadin kai da mutunta juna tsakanin alumma daya, duk da bambance-banbancen su.
Dubban mabiya darikar katolika ne suka taru a port Louis, babban birnin kasar, suna dakon isar shugaban su Fafaroma Francis ya yi jawabi a tsibirin India da ta kasance inda kungiyoyin addinai da na kabilu ke haduwa don tattaunawa.
Josette da ta kasance daya daga cikin masu jiran isowar paparoma, ta ce sama da mutane dubu 3 da dari 5 ne suka fito daga tsibirin Reunion, mai nisan kilometer 175 daga Mauritius.
Ita kuwa Genevieve mai shekaru 47 yar asalin kasar Mauritius ta bayyana wannan taro a matsayin babba, yayin da ta ce haduwarsu da Fafaroma Francis na da matukar muhimmanci.
Kashi 30 cikin 100 na al’ummar Mauritius krista ne, wadanda mafi yawa daga cikin su mabiya darikar katolika ne. saidai Cardinal Maurice Piat, bishop na majami’ar Katolika a babban birnin kasar, ya ce ziyarar shugaban ba ga mabiyansa kadai ba ne, amma ga illahirin alummar kasar masu mabanbantan addini.