Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu, a ranar Lahadin, ya tabbatar da cewa jam’iyyar za ta dawo da shugabancinta a akalla jihohi 25 na kasar nan a shekarar 2023.
Ayu ya bayyana haka ne a wajen wani liyafar godiya da aka gudanar a babban filin wasa na Aper-Aku da ke Makurdi, babban birnin jihar Benue.
“Mun kuduri aniyar kwato akalla jihohi 25 a kasar nan.
“Mun kuduri aniyar karbar Shugabancin kujerun majalisun kasar nan guda biyu – Majalisar Dattawa da na Majalisar Dokokin.
“Za mu dakatar da Yawaitar sauya shekar mambobinmu daga PDP zuwa wasu jam’iyyu.
“Za mu ci gaba da tafiya mai mahimmanci don ƙarin mutane a cikin jam’iyyar,” in ji shi.
Shugaban jam’iyyar na kasa ya kuma bayyana cewa, jam’iyyar PDP a dunkule take, Kuma za ta yi namiji kokari, don samun nasarar lashe jihohin Ekiti da Osun a zaɓen gwamnonin da za su yi nan ba da dadewa ba, yana mai jaddada bukatar jam’iyyar ta masu aminci ta tunkaran kalubalen da ke gabanta.
Ya nuna rashin Jindadinshi kan yadda ’yan Najeriya da ma matasan kasar nan ke kokawa kan yadda gwamnatin tarayya mai ci a yanzu ke gudanar da al’amurorin ta, inda ya bukace su da kada su karaya domin kasar nan za ta sake zama mai daraja.
“Najeriya ba za ta wargaje ba. Najeriya za ta ci gaba da kasancewa a dunkule, mai albarka, mutuntawa da kuma zama a sahun gaba a harkokin duniya.
“Kowane dan jam’iyyar PDP za a tafi da shi.
“Za mu sake gina jam’iyyarmu wato Jam’iyyar PDP za ta yi kokari don lashe zabukan Ekiti da Osun.
Ayu ya kara da cewa “Wadancan kurakuran da mu ka samu na fadi zabe a baya za a gyara su.”
Sai dai kuma ya yi hasashen rugujewar jam’iyyar APC mai mulki a watan Maris zuwa Afrilun shekarar 2023.
Anashi bangaren tun da farko, Bishop na Cocin Diocese dake Birnin Makurdi Bishop Wilfred Anagbe, ya gabatar da jawabinsa a lokacin hidimar cocin wanda gwamnoni hudu suka halarta – na Rivers, Delta, Enugu da Benue.