PDP na zane APC a Zaɓen Osun – Adeyanju ya bayyana inda za’a iya yin Maguɗi cikin Dare
A yayinda sakamakon zaben Gwamnan Jahar Osun yake cigaba da fitowa inda ake kusan ɗaya, Fitaccen mai ƙare haƙƙin Deji Adeyanju ya bayyana cewa Jam’iyyar PDP tana baiwa Jam’iyyar APC kashi a zaɓen.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Tinubu ya bar Osun, zai gana da Kakakin Majalisu na Ƙasa a Abuja
Adeyanju ya gargaɗi PDP akan saurin taya murna ko sakon murna.
A wani sako daya fitar, Mai Fafutukar yace dukkanin abinda ya sanya a gaba shine sakamakon zaɓen Ile Ife, saboda ana iya Maguɗin shi a cikin dare
Ya bayyana irin yadda aka yi Maguɗin zaɓe na sakamakon Shekarar 2018.
Ya rubuta “PDP na zane APC a Osun, Amma kowa ya maida hankali ga sakamakon Ile Ife. Kada ku manta da 2018, wanan shine yanda suka canja sakamakon zabe da daddare.”
Sakamakon daga adireshin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta INEC ya nuna cewa PDP ke kan gaba.