Jami’iyyar PDP ta sake ƙara wa’adin ranar da zata kulle sayar da Form na zaɓen Gwamnan Jahar Ekiti.
Jam’iyyar da ta sanya ranar 14 ga watan Oktoba na Shekarar 2021, a matsayin ranar da zata kulle sayar da form ɗin.
Amma a sanarwar da sakataren yaɗa labaru na Jami’iyyar Kola Ologbondiyan, ya bayyana ranar 22 ga watan Oktoba a matsayin sabuwar ranar da za’a kulle sayar dashi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane 226 sun sake Kamuwa da cutar Covid-19, yayin da 6 su ka mutu a Nigeria
“A dalilin haka, ranar da za’a karɓi takardun takarar da aka cike daga ranar 15 ga watan Oktoba zuwa ranar Juma’a 29 ga watan Oktoba na shekarar 2021.
“Haka zalika, tantance ƴan takarar da zasu tsaya takara zai gudana a ranar Litinin 8 ga watan Nuwamba na shekarar 2021, a Sakatariyar ta ƙasa, Abuja, a yayinda za’a saurari ƙorafi a ranar Litinin 29 ga watan Nuwamba na shekarar 2021.
“Dukkanin ƴan takara, da masu ruwa da tsaki, da mambobin jami’iyyar ana buƙatar dasu marawa wannan al’amari baya,” inji sanarwar.