Jam’iyyar PDP tayi barazana fasa kwai mai wari ga tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo idan har bai fayyace kalaman da ya yi zargin cewa zaben Atiku a matsayin wanda zai tsaya takara a 1999 kuskure ne.
Jam’iyyar PDP ta yi barazanar fasa kwai tare da bayyana wa duniya da ‘yan Nijeriya wane ne Obasanjo cikin sa’o’i 48, idan bai mayar da martani ba.
Kafofin yada labarai sun yi ta juya maganar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a Litinin din makon da ya gabata.
Inda ya ce ya yi kuskure wajen zaben Alhaji Atiku Abubakar a matsayin mataimakinsa a shekarar 1999.
Sai dai shugaban kwamitin amintattu na PDP (BoT), Sanata Walid Jibrin ya ce idan har tsohon shugaban kasar ya kasa fayyace wannan magana cikin sa’o’i 48, “za’a bar jam’iyyar ba ta da wani zabi illa ta tona asirin Obasanjo tare da fadawa ‘yan Najeriya ko wanene shi a zahiri.
Sanata Jibrin wanda ya zanta da manema labarai a Kaduna a ranar Litinin, ya bayyana cewa “PDP na matukar mutunta tsohon shugaban kasa Obasanjo, amma zai yi matukar takaici idan maganar da aka yi masa da kuma dauka a kusan dukkanin jaridun kasar nan gaskiya ne.”
“Maganar da ke cikin wasu na cewa shi, Obasanjo, ya yi kuskure na nada dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku a matsayin abokin takararsa abin takaici ne.” Inji shi.