Jami’iyyar PDP tayi kira ga mahukunta a Najeriya da su gaggauta kame Gwamnan Bankin Kasa CBN, sakamakon yadda ya sanya takalmi wajen murkushe dokokin Aikin Gwamnati a Kasar.
Jam’iyyar Adawar ta ce siyan Fom din tsayawa takara da yayi ya saba da sharuddan da ya kamata ace kowane Ma’aikacin gwamnati ya bi, inda aka jiyo shi ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Wannan na zuwa ne a kasa da awanni 24 da wasu kungiyoyin manoma suka sanar da hada kudi tare da siyawa gwamnan Na CBN Fim din Tsayawa takarar shugaban kasa.
Sakataren wayar da kai na jam’iyyar Debo Ologunagba ne ya yi kiran a yau Asabar, yayi. Da yake ganawa da manema labarai a sakatariyar jam’iyar ta kasa dake Wadata Plaza.
”Jamiyyar mu ta karbi bayanai na sirri dake bayyana cewa Emefele ya Siyi Fom na tsaya takara shugaban kasa, a don haka muke kira ga masu ruwa da tsaki kan a kama shi tare da tuhumar yadda aka yi aka haihu a ragaya,” inji Ologunagba.
Ya ce Dokar CBN ta 2007 sashin na 9 ya ce dole ne gwamnan bankin da mataimakin sa su sadaukar da lokacin su baki daya ga banki, maimakon rabi da rabi.
A dan haka ne jam’iyyar ta bukaci a Kama Emefele tare da tabbatar da an hukunta shi, sakamakon yadda ya sabawa waccan doka.
Comments 1