Jam’iyyar PDP a Gombe ta bukaci wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta haramtawa Gwamna Inuwa Yahaya da mataimakinsa Jatau Daniel tsayawa takarar Gwamna a zaben 2023.
Jam’iyyar ta zargi ‘yan siyasar biyu da mika takardun bogi.
DUBA WANNAN LABARIN: NBC taci Trust TV tarar Miliyan 5
Jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna, Muhammad Barde ne suka nemi a soke zaben a kara mai lamba: FJC/ABJ/CS/1301/2022 tsakanin PDP da wasu mutum biyu da INEC da sauransu.
A cikin takardar sammacin da manyan Lauyoyi biyu na Najeriya, Cif Arthur Okafor, da J.J suka gabatar, a madadin masu shigar da kara, jam’iyyar ta dogara da wasu hukunce-hukuncen kotun koli.
Jam’iyyar PDP ta ce Yahaya da Jatau, bayan da suka ajiye takardar shedar zuwa FORMS EC-9, wato fom din da aka ce sun hada da takardun shaidar karatunsu, anan ne suke zaegin sanya bayanan karya a cikin su.
Wannan, a cewar jam’iyyar, wani mataki ne na hana shiga takara a karkashin sashe na 177(d) da 182(1) (j) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya, 1999 da aka yi wa kwaskwarima.
A cikin shari’ar, masu shigar da kara sun yi zargin cewa Jatau na da sunaye da yawa a cikin takaddun sa, kamar: takardar Firamare dinsa, (Manassah Jatau).
Jam’iyyar PDP ta ce FORM EC-9 kasancewar takardar rantsuwa ce, Yahaya da mataimakinsa, sun yi maganganun karya a ciki, don haka ba su cancanci tsayawa takarar zaben jihar ba.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa ba a sanya ranar da za a saurari karar ba, watakila sai zuwa nan gaba.