PDP ta caccaki Buhari kan yajin aikin ASUU, ta ce Gwamnatin APC ta ɗauki nauyin ta’addanci
Jam’iyyar PDP ta sake tsawatarwa gwamnatin Buhari kan yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke yi.
Babbar jam’iyyar adawa ta yi Allah wadai da lamarin a taron kwamitin zartarwa na kasa a ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tobi Amusan Ta Sake Lashe Kofin Gasar Tseren Diamond League
Sanarwar da Sakataren Yada Labarai na kasa Debo Ologunagba ya fitar, ta koka da gazawar Gwamnatin APC na kawo karshen yajin aiki.
Malamai sun fara kauracewa jami’o’in kasar ne a ranar 14 ga Watan Fabrairu, duk da tayin gwamnati, sun dage kan biyan albashin watanni shida da suka gabata.
Kwamitin jam’iyyar ya zargi Jam’iyyar APC mai mulki da azaba da radadi ga iyaye da daliban jami’o’in gwamnati ke ciki.
PDP ta yi Allah-wadai da “nuna girman kai” da Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya yi wajen magance matsalar tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki su kara hada kai.
Jam’iyyar ta nuna damuwa game da rashin tsaro “sakamakon yadda gwamnatin APC ke da hannu a ciki wanda ke ci gaba da ba da damar ayyukan ta’addanci”.
Kwamitin na NEC ta kuma soki rahoton nadin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na nadin ‘yan jam’iyyar APC masu dauke da kati a matsayin hukumar zabe ta INEC.
PDP ta yi gargadin “Wannan rashin kishin kasa, makirci ne kawai na jam’iyyar APC na yin magudin zabe a 2023 ba tare da ra’ayin ‘yan Najeriya ba.”
‘Yan adawar sun kuma bukaci shugaban kasa ya janye ‘yan jam’iyyar APC da aka zaba a matsayin REC.
Sanarwar ta ce rashin yin hakan na iya haifar da mummunar rikicin siyasa da ka iya yin barazana ga babban zaben shekarar 2023 da kuma kawo cikas ga tsarin mulki.
Kwamitin ayyukan ya kuma yi tir da halin da tattalin arzikin kasa ke ciki, “sakamakon cin hanci da rashawa, rashin hankali, rashin kwarewa da kuma munanan manufofin tattalin arziki”.
‘Yan adawa sun shawarci jama’a da su fitar da APC a shekara mai zuwa su zabi PDP “domin fara babban aikin ceto da sake gina kasarmu”.
A wani labarin kuma: Hare-hare A Makarantu: FG Na Tuhumar Masu Ruwa Da Tsaki Kan Bin Ka’idojin Tsaro
Sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da wasu masu aikata laifuka a makarantun kasar nan, gwamnatin tarayya ta dorawa masu ruwa da tsaki da su sanya ka’idojin tsaro amakarantun da ake da su.
Karamin Ministan Ilimi, Goodluck Opiah, da yake magana a wani taron manema labarai da aka gudanar don bikin ranar kare ilimi daga hare-hare ta 2022, ya dage cewa dole ne masu ruwa da tsaki su aiwatar da ka’idojin tsaron makarantu don kare makarantu daga hare-hare.