PDP ta caccaki Gwamnatin jihar Kwara na shirin kama mambobinta
Kwanaki kadan bayan dage haramcin yakin neman zabe da jam’iyyun siyasar kasar nan suka yi, jam’iyyar PDP ta jihar Kwara ta zargi gwamnatin jihar da shirin cafke ‘yan adawa a jihar.
A wata kakkausar sanarwa da PDP ta fitar a Ilorin ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sama Da Mutane 360,000 Ambaliyar Ruwa Ta Raba Da Muhallansu – NASEMA
Sakataren yada labarai, Prince Tunji Moronfoye, ya yi gargadin illar irin wadannan tsare-tsare, musamman a wannan mawuyacin lokaci na rashin tsaro a kasar baki daya.
Jam’iyyar ta bayyana cewa ta samu bayanan sirri da ke nuna cewa gwamnatin jihar Kwara karkashin jam’iyyar All Progressives Congress na shirin murkushe fitattun ‘yan jam’iyyar adawa a jihar Kwara cikin ‘yan kwanaki kadan.
Ya ce, “Tsarin da ake shirin yi shi ne a bullo da tuhume-tuhume tare da dagewa cewa jami’an tsaro su kama su kuma gurfanar da irin wadannan ‘yan jam’iyyar adawa a kotu.”
Jam’iyyar ta yi kira ga ‘yan Kwara da su ja hankalin gwamnatin jam’iyyar APC da kada ta zafafa harkokin siyasa da wannan mummunar shawara ta murkushe ‘yan jam’iyyar adawa.
“Ya kamata a tuna wa gwamnatin APC ta jihar Kwara irin tabarbarewar tsaro a kasar nan daga yau. Rikici kan ‘yan jam’iyyar adawa bisa zarge-zargen karya na iya haifar da tabarbarewar doka da oda a jihar.
“Za a dage haramcin yakin neman zabe na siyasa nan da ‘yan kwanaki kadan. Mu a jam’iyyar PDP muna fatan gudanar da yakin neman zaben mu cikin yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali wanda jihar Kwara ta yi kaurin suna.
Da yake mayar da martani cikin gaggawa, mai ba gwamnan jihar shawara na musamman kan harkokin siyasa, Bashir Adigun, ya ce “Wannan wata farfagandar PDP ce, wadanda ba su taka doka ba, kada su ji tsoron kama jami’an tsaro.
“Amma gwamnati ba za ta hana ‘yan sanda kama wadanda suka aikata laifi ba,” in ji shi
A wani labarin kuma: Hukumar DSS Ta Ceto Mutane 27 Da Ake Shirin Yin Fataucin Su
Rundunar ‘yan sandan farin kaya (DSS) reshen jihar Kano, ta ceto tare da mika mutane 27 da za a yi safarar su ga rundunar hadin gwiwa ta rundunar ‘yan sandan jihar Kano.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Abdullahi Babale, Kwamandan Hukumar yaki da fataucin bil Adama ta kasa (NAPTIP) shiyyar Kano, ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) a ranar Alhamis din nan a Kano.