An gurfanar da Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrasaq a gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa zarginsa da yin amfani da takardar shaidar kammala karatu ta Yammacin Afirka ta jabu wajen tabbatar da tsayawa takarar Gwamna a zaben 2023 a Jihar.
A karar da jam’iyyar PDP ta shigar a kansa, an bukaci babbar kotun tarayya da ta haramtawa gwamna da jam’iyyar APC shiga zaben gwamna na shekara mai zuwa.
KARANTA WANNAN LABARIN:Kasar China Ta Bude Ofishin ‘Yan Sanda A Najeriya
Sabuwar kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1324/22 an shigar da ita ne a madadin PDP ta hannun wani babban Lauyan Najeriya Cif Paul Erokoro SAN,yace Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC, Abdulrahman Abdulrasaq da Jam’iyyar APC sune a matsayin wanda ake tuhuma na 1 zuwa na 3.
An bukaci kotun da ta yi amfani da sashe na 171 da 285 na kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999 da kuma sashe na 29 na dokar zabe domin soke shirin da gwamnan zai yi a zabe mai zuwa.
PDP ta kuma roki kotun da ta tilasta wa INEC da ta cire gwamna da APC daga cikin jerin sunayen ‘yan takara da jam’iyyu da aka tantance.
Musamman jam’iyyar PDP ta bayyana cewa takardar shaidar kammala karatu ta WAEC da gwamna ya mika ta hannun jam’iyyar APC domin ta taimaka masa wajen neman ilimi kamar yadda sashe na 177 na kundin tsarin mulkin Najeriya shekarar 1999 ya tanada na jabu ne ba nasa ba.
A halin da ake ciki, Mai shari’a Inyang Edem Ekwo ya sanya ranar 28 ga watan Oktoba domin sauraron karar.
A wani labarin kuma, Bayan Janye Yajin Aikin ASUU: Jami’ar Obafemi Awolowo Ta Sanya Ranar Cigaba Da Karatu
Hukumar gudanarwar Jami’ar Obafemi Awolowo dake garin Ile-Ife, a ranar Talata, ta bayyana ranar da za a ci gaba da gudanar da
harkokin karantun ta. Kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito
Hukumar gudanarwar ta dai sanya ranar Alhamis, 20 ga watan Oktoban shekarar 2022 a matsayin rarar komawa makarantar.