By Abbas Yakubu Yaura
Jam’iyyar PDP ta bayyana Gwamnan Jihar Sakkwato kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP, Aminu Tambuwal a matsayin shugaba mai tawali’u, mai kwazo da kuzari, yayin da ta taya shi murnar cika shekaru 56 a duniya.
Wannan na zuwa ne a wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ya fitar ranar Litinin mai taken ‘PDP na taya Gwamna Tambuwal murnar cika shekaru 56.
Ologunagba ya ce, “Gwamna Tambuwal fitaccen dan kishin kasa ne kuma jajirtacce dan dimokradiyya wanda tsawon shekaru a matsayinsa na kakakin majalisar wakilai kuma a yanzu ya zama gwamnan jiha sau biyu, yana ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen ganin an samu hadin kai, zaman lafiya da ci gaban mu.
“A matsayinsa na Kakakin Majalisar Wakilai, Gwamna Tambuwal, da kyakykyawan salon siyasa, ya zurfafa al’adarmu ta dimokuradiyya ta hanyar tabbatar da gaskiya da gudanar da mulki mai inganci ta hanyar karfafa ka’idar raba madafun iko tare da tabbatar da ‘yancin kan majalisa kamar yadda aka tanada a shekarar 1999 a Kundin Tsarin Mulkin (kamar yadda aka gyara).
“Kamar yadda Gwamna Aminu Tambuwal ke ci gaba da nuna jajircewarsa wajen kyautata rayuwar al’ummarsa kamar yadda yake bayyana a ayyukan raya kasa a sassa masu muhimmanci da suka hada da ilimi, kiwon lafiya, noma, ababen more rayuwa da raya birane da karkara da sauransu.”
Ya kara da cewa a matsayinsa na shugaban kungiyar Gwamnonin PDP, Tambuwal ya ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da hadin kai, kwanciyar hankali, ci gaban da kuma nasarar zaben PDP.
Ologunagba ya kuma ce jajircewar Tambuwal wajen samun nasarar yunƙurin sulhuntawa a jam’iyyar PDP ya kasance muhimmiyar ma’ana wajen mayar da jam’iyyar a matsayin dandalin ‘yan Nijeriya domin ceto da sake gina al’ummar ƙasar daga halin kunci.
Sannan yace “Iyalan PDP na taya Gwamna Tambuwal murnar wannan gagarumin biki tare da yi masa addu’ar Allah ya kara masa shekaru masu yawa a cikin koshin lafiya domin ci gaba da yi wa kasarmu da jama’a baki daya hidima,” in ji sanarwar.