Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce ta aika da sunayen wadanda za su yi takara a karkashin jam’iyyar a zaben kananan hukumomi da za a yi. Inda suka ce tuni suka mika sunayensu ‘yan takararsu da shugaban hukumar shirya zabukan na jihar, KANSIEC, Farfesa Garba Ibrahim Sheka.
Idan ba ku manta ba, da jam’iyyar PDP din a Kano ta ce ba za ta shiga cikin jerin jam’iyyun da za su tsaida ‘yan takara ba.