Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta ce kashe-kashen ‘yan Nijeriya a kasar Afrika ta Kudu bisa wariya da ‘yan kasar ke nuna musu, abin tir ne da Allah-wadai. Jam’iyyar PDP din ta ce tana tir bisa kashe ‘yan Nijeriya da sauran baki da wadansu bata gari ke yi a kasar ta Afrika ta Kudu.
PDP ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Sakataren yada labaran jam’iyyar Kola Ologbondiyan, ya sanyawa hannu, inda ya ce; tabbas kashe bakin a Afrika ta Kudu abin tir ne, kuma ba abin a yafe bane ko a karbi uzuri.
Ologbondiyan ya yi kira ga ‘yan majalisa da su ceci ‘yan Nijeriya a Afrika ta Kudu, ta hanyar gudanar da zama na musamman domin tattauna batun ‘yan Nijeriya a Afrika ta Kudu.