Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya shaida wa magoya bayan jam’iyyar da ‘yan Nijeriya cewa jam’iyyar za ta lashe gwamnoni 25 ko fiye a zaben 2023 kamar yadda ta saba yi a baya.
Ayu ya bayyana haka ne bayan wata ganawar sirri da ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar daga jihohi 34 da ke fadin kasar nan a ranar Laraba a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Tsare Wani Mutum Bisa Yiwa Wata Yarinya Fyade
Ayu ya ce ’yan takarar gwamnan sun gana da wasu mambobin kwamitin ayyuka na kasa domin bayyana damuwarsu a jihohinsu daban-daban kan kokarin da suke yi na cin zabe a jihohinsu.
“’Yan takarar sun zo sun bayyana damuwarsu a jihohinsu daban-daban. Ya yi mana bayani kan kokarin da suke yi a jihohinsu daban-daban na ganin sun ci zabe.
“Muna son dawo da gwamnonin jihohi kusan 25 ko fiye kamar yadda muke da su. Don haka yanayi a cikin jam’iyyar yana da kyau.
“Mun kuduri aniyar cewa ba wai kawai mun samu nasara a matakin kasa ba, jihohi da majalisun kasa, da gwamnonin jihohi, muna son dawo da gwamnoni kusan 25 ko sama da haka kamar yadda muke da su. Don haka yanayi a cikin jam’iyyar yana da kyau.
A WANI LABARIN KUMA: Gwamnatin Tarayya Tayi Ƙarin Girma ga Jami’an Kashe Gobara 2,382