By Abbas Yakubu Yaura
Kwamitin ayyuka na kasa na jam’iyyar PDP ya sanar da cewa zai gabatar da takardar shaidar cin zabe ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Atiku Abubakar.
Atiku ya lashe tikitin tsayawa takarar shugaban kasa na jam’iyyar ne a babban taron kasa da aka gudanar a Abuja a ranakun 28 zuwa 29 ga watan Mayun 2022 bayan ya samu kuri’u 371.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Bauchi Ta Sassauta Dokar Hana Fita Ta Sa’o’i 24 Data Sanya Kan Rikicin Yelwa Zuwa Sa’oi 12
Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce ana sa ran dukkanin gwamnoni, ‘yan takarar gwamna, masu neman shugabancin kasa, mambobin kwamitin amintattu, ‘yan majalisar dokoki ta kasa, sauran ‘yan takarar jam’iyyar da kuma duk masu ruwa da tsaki za su halacci bikin na musamman.
Sanarwar ta ci gaba da cewa taron zai gudana ne a ranar Laraba 1 ga watan Yuni 2022 da tsakar rana a sakatariyar PDP ta kasa da ke Abuja.
A WANI LABARIN KUMA
An yi kira ga jami’o’i da gwamnatin tarayya da su hada karfi da karfe su hada kai domin daliban Najeriya su bar tituna su koma karatu.
Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa a majalisar wakilai ta kasa, Orji Uzor Kalu, ne ya yi wannan roko a yau Talata, cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Sanatan ya kuma jajanta wa daliban Najeriya “wadanda ba sa zuwa makaranta saboda yajin aikin ASUU da suke yi”.
Ya ce, “Ina kira ga jami’o’i da gwamnatin tarayya da su hada karfi da karfe domin dalibanmu su bar tituna su koma karatu.”
Sanatan yayi waiwayen baya inda ya ce, “A lokacin da nake Gwamnan Jihar Abia (199-2007), karatun Firamare zuwa Jami’a (a Jihar) an yi shi kyauta kuma mai araha.
“Ya kamata jihohi da gwamnatin tarayya su mai da hankali sosai kan ilimi. Babu wani alhaki ga kowace gwamnati ta ki kula da fannin ilimi.”
Ya kara da cewa, “Yajin aikin da ba a gama ba yana haifar da tsaiko wajen kammala yaye dalibai tare da sassauta tsare-tsaren rayuwarsu da harkokin rayuwarsu”.