• Jam’iyar PDP ta yi barazanar kwace mukaman wadanda suka sauya sheka zuwa wata jam’iyar.
• Jam’iyar PDP ta kuma koka kan tsadar kudin Fom da hukumar zaben jihar ta sanya.
• Ta shawarci Hukumar da ta maida kudin Fom din kyauta
Jam’iyar Adawa ta PDP reshen jihar Nassarawa, ta yi barazanar daukar dokar da ta dace, kan zababbun masu rike da kujerun siyasa, wadanda su ka sauya sheka zuwa wata jam’iya, inda kuma ta bukaci su, da su yi gagawan aje mukaman su, ko su fuskanci hukuncin doka.
Shugaban jam’iyar PDP reshen jihar Comared Francis Orogun ne, ya bayyana hakan, jim kadan bayan kammala taron kwamitin gudanarwar jam’iyar a jiya Talata, a garin Lafiya .
KARANTA WANNAN LABARIN: Zamu Kwatowa Jam’iyar APC Yancin su, inji wani Lauya
Inda ya bukaci wasu daga cikin yan majalissun dokokin jihar, da a ka zabe su a inuwar jam’iyar PDP, kuma su ka sauya sheka zuwa Jam’iyar APC, da su aje mukaman su, kafin doka ta yi aiki a kan su.
A cewar shi, wadanda aka zabe su a cikin inuwar jam’iyar PDP, suna da damar barin jam’iyar, amma ba tare da tafiya da hakkokin ta ba.
Kazalika jam’iyar ta ce, zata iya shiga zaben da za’ayi a ranar 6 ga watan Octoban a jihar, inda kuma ta bukaci mambobin ta, da su wayar da kan al’uma a kan yan takarkarun su, da su ke neman wasu kujerun siyasa.
Bugu da kari, Shugaban jam’iyar ya koka kan tsadar kudin Fom, da hukumar zabe Mai zaman kanta ta jihar NASIEC, ta sanya kan kujerun zabubbukan da za’a gudanar.
Idan za’a iya tuna wa, a ranar Laraba 7 ga watan Yulin shekaran nan ne, Shugaban NASIEC Ayuba Wanda,i ya bayyana cewa, hukumar ta sanya kudin kujeran Kansila a kan kudi naira 200,000, inda kuma kudin kujeran Ciyaman ya kai Naira 500,000.
Orogu ya ce, a irin wannan yanayi da mutanan jihar ke ciki, kudin Fom da aka sanya bai dace ba, kuma ya yi tsadar gaske.
A karshe shugaban jam’iyar ta PDP ya shawarci Hukumar zaben jihar, da ta mai da kudin Fom din kyauta, ko kuma ta rage adadin kudin.
Comments 1