Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya yi watsi da kididdigar yanar gizo da ta sanya Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour a gaban Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC da kuma dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
Sule ya yi ikirarin cewa sukar Obi, wanda tsohon gwamnan jihar Anambra ne, da gwamna mai ci, Charles Soludo ya yi, wanda ya rage darajar Obi a matsayin dan takarar shugaban kasa da kasa da kobo 10.
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalisar Dattijai Ta Ki Amincewa Da Bukatar Maidawa Gwamantin Jihar Kebbi Naira Billiyan 6.7
Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake gabatar da shirin siyasa a Gidan Talabijin na Channels mai suna Politics Today.
Sule ya ce gwamnan jihar Anambra na yanzu inda Peter Obi ya kasance gwamna shine wanda ya dace ya fadi abinda ya faru a zamanin Peter Obi a jihar.
“Don haka, idan za ku je Anambra, ku dubi abin da gwamnan Anambra (yana cewa). Suna jam’iyya daya. Ba wai sun canza jam’iyyu ba ne. Peter Obi ne ya canza jam’iyya, amma jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) daya ce.
“Don haka, idan ka je ka ga abin da yake fada a yau game da Peter Obi, ba za ka sayi Peter Obi kan kobo 10 ba.”
Ya kara da cewa, ba bu yadda za a yi a kwatanta Tinubu da Obi, yana mai cewa Tinubu ya kyautata tattalin arzikin Legas a yau fiye da jihar Anambra.
A wani labari kuma, ‘Yan Majalisar Kano Sun Yi Alkawarin Hanzarta Doba Dokoki
Majalisar dokokin jihar Kano ta yi alkawarin hada hannu da gwamnatin jihar da sauran kungiyoyi wajen fitar da dokokin da za su inganta rayuwar al’ummar jihar da zamantakewar da kuma tattalin arzikin jihar.
Kakakin majalisar, Hamisu Ibrahim Chidari, ne ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana bude wani taro na kwanaki uku da gwamnatin jihar Kano da majalisar dokokin jihar 37 suka shirya a Abuja ranar Laraba