Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Dumebi Kachikwu, ya bayyana cewa babu bambanci tsakanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LP), Peter Obi, dana jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da kuma na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.
Kachikwu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV’s a cikin shirin Politics Today.
KARANTA WANNAN LABARIN: FG Ta Yi Rashin Nasara Kan Karar Data Shigar Na Mika Wani Dan Kasuwa Zuwa Amurka
Ya ce ‘yan takarar shugaban kasa uku na cikin tsohon tsarin siyasa.
Ya ce, “Abin da ya sa ba ma son haduwa da Peter Obi, jam’iyyar Labour, mu gan shi a cikin kananan jam’iyyu shi ne kawai saboda babu bambanci tsakanin Peter Obi, Atiku Abubakar da Asiwaju. Suna cikin tsohon tsarin siyasa. Mutane ne da suka rike mukamai.”
“Duk ɗaya ne kuma ba su da wani abin da za su iya bayarwa. Babu wani dalili da zai sa mu ce mun taru ne da manufar mulki.”
“Ba na cikin wannan domin ina neman mulki da kyakkyawan nufi. Ina cikin wannan saboda kasata na matukar bukatar canji da ceto.”
“Don haka idan za mu ce muna neman mulki, muna la’akari da duk wata daidaitawa kawai don samun mulki. Wannan ba shine dalilin da ya sa muke cikin wannan ba.”
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Jarumin Kannywood Na Shirin Kwana Casa’in, Kafi Gwamna, Ya Rasu
Allah yayi wa jarumin kannywood na cikin shirin kwana casa’in Alhaji Umaru Malumfashi wanda aka fi sani da “KAFI GWAMNA” rasuwa.
Bayanan rasuwar tasa na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daya daga cikin jaruman masana’antar ta kannywood Abba El-Mustapha ya fitar ta kafar sada zumunta ta Instagram a daren yau Talata 27 ga watan Satumba 2022.