Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, a ranar Lahadi ya gana da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Obi ya gana da jigon na jam’iyyar PDP a gidansa da ke Legas.
Wani na hannun daman Fayose Lere Olayinka ne ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a dandalinshi na sada zumunta.
Kofin Aiteo 2022: Gawuna Ya Yabawa KKK Kano Pillars Yayin Da Suka Nasara
Lere Olayinka ya raba hotunan Fayose da tsohon gwamnan jihar Anambra, tare da taken: “Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour party, Peter Obi ya ziyarci tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose a gidansa na Legas a yau.”
Idan zaku iya tunawa, Obi ya fice daga PDP ne bayan samun tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, inda ya zama dan takarar jam’iyyar.
Har yanzu dai ba a san makasudin ganawar Obi da Fayose ba, amma akwai jita-jitar cewa tsohon gwamnan Ekiti na shirin yi masa aiki a zaben 2023.
A baya Fayose ya bayyana cewa ba zai goyi bayan dan takarar PDP, Atiku Abubakar ba, kan yadda shi da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP suka yi wa Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas mubaya’a, bayan zaben fidda gwani na jam’iyyar.