By Abbas Yakubu Yaura
Wani mutum mai suna Samuel Mathew ya kashe matar sa ‘yar shekara 23 mai suna Mercy Samuel a garin Jos ta jihar Filato.
An ce marigayiyar tana zaune tare da mijinta a kan hanyar Vom a karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato a lokacin da lamarin ya faru.
An tattaro cewa mijin Mercy ya farka cikinta ne kuma ya yanke mata hanjin, wanda a yanzu haka ya gudu, yayin da aka samu rashin jituwa a daren Lahadi.
An garzaya da ita Asibitin Koyarwa na Jami’ar Bingham da ke Jos inda ake ta faman neman kokarin ceto ranta amma daga bisani ta rasu a ranar Laraba.
Jami’ar da ke kula da harkokin mata ta jiha, WRAPA, Jummai Madaki, wadda ke kokarin ganin an tallafa wa marigayiyar Mercy, kafin rasuwarta, ta bukaci dukkan masu hannu da shuni da su tashi tsaye wajen tabbatar da adalci ga marigayiyar.
Madaki ta bayyana cewa, “A baya an taba samun tashin hankali a kanta kamar yadda ‘yan uwanta suka tabbatar amma dangin mijin sun musanta faruwar hakan. Mutumin ya tsaga cikinta ya cire mata hanjin sannan ya yanke kafin ya bace da wayarta dan kada ta samu damar kiran taimako.
“Suna zaune ne a wani karamin gida don haka ina mamakin dalilin da ya sa ba wanda ya ji ihun ta, an ce mana taimako bai zo ba sai da sanyin safiyar ranar Litinin aka garzaya da ita asibiti aka sanya mata iskar oxygen. Wani mai ba da labari ya kira ya sanar damu abin da ya faru.
Amma abin mamaki ba a kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda ba. Iyayenta sun shaida mana cewa ko a shekarar da ta gabata tana gida saboda wasu matsaloli amma mutanen mijin sun zo bara sai ta koma”.
Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban jama’a, Rebecca Sambo, wadda ita ma ta ziyarci gidan iyalan mamacin da ke Gyel a Jos ta Kudu, ta bayyana bakin cikinta game da faruwar lamarin tare da tabbatar wa ‘yan uwa cewa ba za a share maganar a karkashin kafet ba, tana mai cewa, “’Yan sanda an sanar dasu kuma an fara daukar mataki don tabbatar da samun adalci ga yarinyar.”
Ta shawarci mata da su rika fadin albarkacin bakinsu da zarar sun gane akwai wani hadari a cikin aurensu, kada su ba da kansu ga kashe-kashe da mazaje masu tayar da zaune tsaye suke yi, sannan ta umurci mata da su tunkari Tebura da ke ofisoshin ‘yan sanda su kai rahoto ga jami’an da suka shafi cin zarafin mata.