Kungiyar Mawaka ta Nijeriya (PMAN) ta shawarci matasan Nijeriya da su guji tashin hankali su rungumi zaman lafiya domin tabbatar da zaman lafiya a cikin kasa.
Mista Dovie Mena, wanda aka fi sani da Baba 2010, Shugaban kungiyar masu ruwa da tsaki na PMAN reshen Abuja shi ne ya fadi hakan lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Abuja a yau Alhamis.
Mena, fitaccen mawaƙin Afro-highlife, ya ce, “Dole ne matasan Nijeriya su guji tashin hankali su ɗauki kansu a matsayin jagororin a gaba”.
Ya ci gaba da cewa; “Ya kamata su kuma yi amfani da basirar su wajen kyautata martabar Nijeriya wacce kalubalen tsaro a yau ya sanya martabar ya yi kasa”.
“Matasan mu su yi koyi da mashahuran mutane kamar Davido, Wizkid, Burna boy da sauransu, waɗanda suka sami damar yin amfani da tasirin kiɗa don nuna al’adun gargajiyar Nijeriya masu albarka a duk duniya.”
Ya ce kungiyarsu ta yanke shawarar tallafawa Gwamnatin Tarayya kan yaki da kalubalen tsaro a kasar.