A yau juma’a Mai horas da kungiyar kwallon kafa Paris Saint-Germain Mauricio Pochettino, ya sabunta kwantiragin shi na cigaba da zama a kungiyar da shekara daya, Wanda hakan ya sa, zai cigaba da zama a kungiyar har nan da shekarar 2023
Dan Kasar Ajantina ya karbi ragamar horas da kungiyar ce, tun bayan da PSG ta sallami Tsohon Kocin na ta Wato Thomas Tuchel, a watan Janairun shekarar nan.
Sai dai kungiyar kwallon kafa ta PSG ba ta yi nasarar lashe gasar kofin na kasar Faransa ba, a kakar wasar da ta gabata.
” Ina matukar cikin farin ciki da kai na, da kuma abokan aiki na” Kamar yadda Pochettino ya bayyana, wanda kuma tsohon Kaftin din kungiyar ce ta PSG.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Zamfara ta bai wa iyalan wadanda aka kashe Naira Milliyan 15
” Abu ne Mai matukar amfani da muka sami yarda daga hukumomin kungiyar, kuma za mu yi, iya iyawar mu, domin mu faranta wa magoya bayan kungiyar rai, ta yadda zasu alfari da Paris Saint-Germajn.” A cewar shi.
” Hakan yasa zamu zage damtse wajan cinma manufofin mu tare, kuma shekaru ashirin da su ka gabata, na rike wa kungiyar Kambun Kaftin, ga shi kuma a yau ni ne Mai horas da kungiyar, wannan mafarki na ne ya zamo gaskiya” inji Kocin na PSG.
Comments 1