Bayanai sun tabbatar da cewa; dan wasan tsakiyarnan na Faransa Paul Pogba, mai shekara 27 ya fasa zuwa ko’ina, inda ake sa ran zai sabunta zamansa a kungiyar ta Manchester United har na tsawon shekara biyar kamar yadda kafar watsa labarai ta SUN ta labarto.
Haka zalika, suma Bayer Leverkusen ta amince da matakin da dan wasan Jamus Kai Havertz, mai shekara 21, wanda ya dauka na komawa kugiyar Chelsea amma tana so ta jinkirta tafiyarsa sai karshen watan Agusta.
Sannan kungiyar Manchester City tana son dauko dan wasan Ajax da Argentina Nicolas Tagliafico, mai shekara 27, a lokacin bazara kamar yadda rahoton BBC ya tabbatar.