Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta bayyana dan takarar jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Musa Aga Avia, a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani na Jos North/Bassa.
Da yake sanar da sakamakon zaben a cibiyar tattara sakamakon zaben da ke Jos, Dokta Yinka Oyerinde, daga sashen nazarin kimiyyar na’ura mai kwakwalwa ta Jami’ar Jos, ya ce dan takarar jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 40,343 inda ya kayar da abokin hamayyarsa Adamu Muhammad Alkali na jam’iyyar Peoples Redemption Party. (PRP), wanda ya samu kuri’u 37,757.
Dokta Oyerinde ya ce dan takarar jam’iyyar APC, Joseph Abbey Aku, ya samu kuri’u 26,111 Wanda Kuma Hakan yasa ya zo na uku a zaben.
Wakilin jam’iyyar PRP ya ki sanya hannu a takardar sakamakon zaben, inda ya ce an tafka kura-kurai a cibiyar tattara sakamakon zaben na Tudun Wada/Kabon.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an gudanar da zaben ne domin cike gurbin kujerar mazabar bayan rasuwar marigayi Haruna Maitala, wanda ya rasu a ranar 3 ga Afrilu, 2021, a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi a hanyar Abuja zuwa Jos.
Comments 1