Kungiyar PSG ta sanar da daukan dan wasan kasar Morocco Achraf Hakimi a kan kudi yiro milliyan 60.
Mai tsaran bayan kasar Marocco ya shafe kakara wasar da ta gabata ne a kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan, inda ya taimakawa kungiyar, wajan lashe gasar Serie A na kasar Italiya.
Dan wasan mai shekara 22 ya sanya hannun kan yarjejeniyar shekara biyar a PSG, Wanda ya kasance dan wasa na biyu, da kungiyar ta siya bayan Georginio Wijnaldum a kakar wadannan.
“Ina matukar farin ciki da wannan rana” kamar yadda Achraf ya bayyana a shafin yanar gizo na kungiyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda sun kubutar da Mai ba Gwamna shawara
“Bayan kasar Sifaniya, Jamus, da Italiya, kungiyar Paris Saint-Germain ta bani damar sake gwada wani sabon gasa, tare da daya daga cikin manyan kungiyoyin duniya, don haka na zaku na ga abokan wasana, Magoya baya da kuma sauran ababen sha’awa a Filin wasa na Parc Des Princes.” Inji shi