Kungiyar PSG ta lallasa Barcelona da 4-1 a karawar farko da suka yi a zagayen gasar zakarun Turai na biyu, da ya kunshi kungiyoyi 16.
Tauraron PSG Kylian Mbappe ne ya ci kwallaye 3, yayin da Moise Kean ya ci 1.
Karo na 11 kenan da kungiyoyin ke karawa da juna a gasar ta Zakarun Turai, inda Barcelona ta samu nasara sau 4, PSG ma sau 4, yayin da kuma aka tashi kunnen doki a wasanni 3.
Kafin karawar ranar Talatar nan, wasa na karshe da suka fafata da juna shi ne na kakar wasa ta 2016/2017, inda a wasan farko PSG ata lallasa Barcelona da 4-0 a birnin Paris, yayin da kuma a Spain Barcelonan ta lallasa PSG da 6-1.