PTA ta Ƙaryata batun bayar da dubu Goma-Goma don kawo karshen yajin aikin ASUU
Kungiyar iyayen yara ta Najeriya ta karyata maganar cewa za ta bayar da gudunmawar Naira 10,000 kowannensu ga daliban Najeriya, ga kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, domin kawo karshen yajin aikin na watanni 6.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa Alhaji Haruna Danjuma ya fitar, ya nesanta kungiyar daga wannan ikirarin..
KARANTA WANNAN LABARIN: Sojojin Najeriya sun ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su a Birnin Gwari
Ya yi bayanin cewa PTA ba ta da masaniyar wannan furucin, ya kuma gargadi wani ko wasu jama’a da su yi amfani da sunan su wajen kawo rudani a kasar nan.
A cewar sa, “Ba mu da hannu cikin wata sanarwa da ta shafi biyan kudi ga ASUU domin su janye yajin aikin da suke yi.”
Ya kara da cewa, “A matsayinmu tun da aka fara yajin aikin, shi ne kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya su cimma matsaya, wato a kawo karshen yajin aikin amma ba wai a ba da kudi don biyan ASUU ba.
Yayin da yake kira ga gwamnatin tarayya da ta saurari bukatar ASUU, shugaban PTA ya kuma roki gwamnatin tarayya da ta kubutar da duk daliban makarantar sakandare da aka yi garkuwa da su da sauran ‘yan Najeriya a fadin kasar nan da ke hannun ‘yan bindiga.
Danjuma ya koka kan halin da ake ciki yanzu a garin Yawuri, inda har yanzu haka Ɗalibai mata da aka sace suna hannun ‘yan bindiga sama da kwanaki 400.
A Wani Labarin kuma:Sojojin Najeriya sun ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su a Birnin Gwari
Rundunar Sojin Najeriya a ranar Juma’a ta ce Jami’an tsaro sun ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa dasu a ƙaramar Hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.