Qatar Zata gina Rukunin Gidaje ga Wanda Iftila’in Ta’addanci ya shafa a Sokoto — FG
Ƙaramin Ministan, Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Kasa Clem Agba yace Gidauniyar Bada Tallafi ta Qatar ta shirya gina rukunin gidaje ga waɗanda iftila’in ta’addanci ya shafa a Jahar Sokoto.
Ya bayyana haka a Abuja a lokacin da yake sanya hannu tsakanin Gwamnatin da Gidauniyar ta Ƙasar Qatar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilan da suka sanya na Kori Malamai 1000 — Inji Soludo
Yace yarjejeniyar an ƙulla ta ne domin baiwa Ƙungiyar damar zama ɗaya daga cikin Ƙungiyoyi masu bada tallafi na Ƙasashen Waje.
Agba yace hakan zai bada dama Ƙungiyar ta gudanar da aikin bada tallafin jinƙai, da wasu cigaba a ƙarƙashin Jagorancin Ofishin Jakadancin Qatar a Najeriya.
Comments 1