Mazauna birnin tarayya Abuja sun bayyana ra’ayoyinsu game da kidayar al’ummar kasa a shekara mai zuwa da aka shirya gudanarwa a watan Afrilun 2023.
Mista Soboma West, mazaunin yankin Lugbe, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa, wannan kidayar na da muhimmanci kuma tana bukatar goyon bayan dukkan ‘yan Najeriya.
“Najeriya a matsayinta na kasa tana bukatar tsara yadda ake rabon albarkatun kasa da yadda ake tafiyar da shi domin ingantaccen ci gaban kasa.”
Ya kuma ce ” kidayar wani aiki ne mai matukar amfani da ke taimakawa wajen sarrafa albarkatun kasa.”
KARANTA WANNA: https://dimokuradiyya.com.ng/kakar-dan-takarar-gwamnan-jihar-kano-na-jamiyyar-nnpp-abba-gida-gida-ta-rasu/
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Mista Favor Ehiogu wani matashi dan Najeriya kuma mazaunin gidajen gwamnatin tarayya, Lugbe ya kuma ce, idan alkaluman da aka tattara za a yi amfani da su yadda ya kamata, to ya zama dole ayi.
“Wannan zai baiwa shugabanninmu kyakkyawar mayar da hankali kan yadda za a tunkari batutuwa daban-daban tare da ware abubuwan da suka dace,” in ji shi.
Mista Chindeu Nwagou ya ce “Najeriya na bukatar ta zama kasa mai inganci kuma kidayar ya zama dole wajen tsarawa da aiwatar da ci gaban tattalin arziki.”
Nwagou ya ba da shawarar a yi amfani da kididdigar da aka tattara domin kawo sauyi mai kyau a kasar.
“Kidayar 2023 za ta kasance cikakkiyar kididdigar al’ummar Najeriya wanda zai zama kidayar kasa ta biyar a kasar tun bayan samun ‘yancin kai.”
“Zai zama kidayar jama’a ta farko da aka gudanar tun bayan kidayar jama’a a shekarar 2006,” in ji shi.
(NAN)