A jiya Alhamis ne aka kawo karshen zagayen kusa da na kusa da na Karshe a gasar zakarun nahiyar turai ta Europa, inda Kungiyoyi huɗu suka tsallaka zuwa zagaye na gaba.
Kungiyoyin su ne Arsenal da Manchester United dukkannin su daga Kadar Ingila sai Kuma AD Roma daga Italiya yayin da Villareal ta daga Spaniya ta yi rufa ido.
Ita Ƙungiyar Manchester United United ta samu zuwa wannan zagaye ne bayan lallasa Granada daga Kasar 4:0 gida da waje.
A hannu guda kuma takwararta ta Arsenal ta chaskale Slavia Prague ne kwallaye 5:1 ɗaya gida da wajen.
Ita Kuwa Villareal ta yi kukan kura ne kan Dynamo Zagreb da kwallaye 3:1 gida da waje, yayin da AS Roma ta ta tsallake rijiya da kundum baya hannu Ajax da kwallaye 3:2 Jimilla.
Da wadannan Sakamako dai yanzu haka Kungiyar Arsenal za ta haɗu da tsohon Mai horas da ita Kenan Unai Emery, yayin da tsofin yan wasan Manchester United Henrikh Mkhitaryan za su iya nuna wa tsohuwar Kungiyar tasu cewa ruwa na maganin dauɗa.
Dukkanin wadannan karawa za a yi su ne a ranar Alhamis 29 ga watan Afirelun da muke ciki, yayin da zagaye na biyu kuma zai gudana a ranar Alhamis 6 ga watan Mayu gobe.