Rabaran Fr. Joseph Danjuma Shekari wanda yan bindiga suka yi garkuwa da shi a sanyin safiyar jiya Litinin ya shaki iskar yanci.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban rukunin Cocin Katolika na Kafanchan Rabran Fr. Emmanuel ya fitar
An dai yi Garkuwa da Rabaran Fr Shekari ne a Cocin sa dake Ikulu Park na karamar hukumar Kauru dake jihar Kaduna.
“Zuciyoyinmu cike da Farinciki, Muna farin cikin sanar daku cikin yabon Ubangiji cewa, Dan uwanmu Rabran Fr. Joseph Danjuma Shekari ya Sami yanci Daga Hannun Yan bindigan da sukayi Garkuwa da shi”
“Fr.Shekari ya Shaki yancin ne da misalin karfe 10:30 na daren jiya Litinin, 7 ga watan Fabarairun shekarar 2022.”
A lokacin samamen Yan bindigan sun kashe daya daga cikin Mai wa Faston girkin abinci.
“Kana Cocin ta Kuma yi addu’ar Neman Rahama ga wacce aka kashe sanadiyar harin” inji snaarwar.