Shahararen ɗan wasannan nan da ake kira da sarkin taɓo a duniyar tennis wato Rafael Nadal ya zamo zakara a gasar French Open da aka kammala a can ƙasar Faransa. Ya zamo zakara ne bayan ya lallasa takwaransa kuma abokin hamayyarsa wato Novac Djokovic a wasan ƙarshen da suka fafata daci 6-0 da 2-6 da kuma 5-7.
‘Yan wasan guda biyu Nadal da Djokovic hamayyace mai zafi a tsakaninsu duba da yadda kowa yake ragargazar kowa a gasar, sai dai za a iya cewa kowa akwai a irin gasar da yake dukan kowa idan aka haɗu. Wannan shine karo na 13 a tarihi da Rafael Nadal yana lashe gasa mai daraja ta farko wato Grand Slam ta French Open, jimilla dai ya lashe French Open da Australian Open da U.S Open da Wimbledon Open guda 20 kenan a tarihi.
Nadal ya lashe gasar French Open sau 13, wato a 2005 da 2006 da 2007 da 2008 da 2010 da 2011 da 2012 da 2013 da 2014 da 2017 da 2018 da 2019 da kuma 2020.
Yaashe gasar Australian Open sau 1 a shekarar 2009.
Ya lashe gasar U.S Open sau 4 a shekarun 2010 da 2013 da 2017 da kuma 2019.
Ya lashe gasar Wimbledon Open sau 2 a shekarun 2008 da kuma 2010.
Nadal da Djokovic wannan itace haɗuwarsu ta 56 a tarihi amma a gasa daban-daban, sai dai za a iya cewa Djokovic yafi samun nasara, amma kuma daga cikin gasussukan da ake fafatawa a wasan French Open sun haɗu sau 8 inda Nadal ya doke Djokovic sau 7 shikuma ya dokeshi sau 1.
Haka a wasan tennis na ciyawa sun haɗu sau 4 kowa ya samu nasara akan abokin hamayyar sa sau 2, sannan kuma a gasar U.S Open sun haɗu sau 3 inda Nadal ya lashe Djokovic sau 2 shimuma ya lashe Nadal sau 1. Amma kuma a gasar Australian Open sun haɗu sau 2 inda Djokovic ya lashe Nadal. Sannan a gasar Wimbledon sun haɗu sau 3 inda Djokovic ya lashe shi sau 2 shikamua Nadal ya lashe Djokovic sau 1.
Amma a wasan da ake kira na yumɓu Nadal ya lashe Djokovic sau 18 inda shikuma Djokovic ya lashe Nadal sau 7, haka zalika a wasan da ake kira da Hard Courts sun haɗu sau 27 inda Djokovic ya ragargaza Nadal sau 20 shikuma Nadal ya samu nasara akan Djokovic sau 7.
Haka zalika za a iya cewa ta tabbata cewar Rafael Nadal shine zakaran gasar French Open na shekarar 2020 inda za a iya cewa ya yiwa abokin hamayyar nasa kayen rabani da yaro wanda daman yafi kowa yawan lashe gasar mai taken Roland Garros wato French Open.