Mai Magana da yawun shugaban Kasa Mallam Garba Shehu ya bayyana dalilin da ya sabbaba shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai damka ragamar kasar nan ga mataimakin shi Farfesa Yemi Osinbajo.
A Halin da ake ciki yanzu haka Buhari yana chan birnin Landan inda ake duba lafiyar shi.
Da yake magana da tashar Talabijin na Channels, Garba Shehu ya ce dalilin da ya sa shugaban kasar ya dauki matakin tafiya ba tare da barin ragamar ta wa Osinbajo ba shine ba shafe wani tsawon lokaci ba ne a chan kasar waje.
Don haka ya ce yana chan din zai iya kula da komai dake tafiya a kasar.
“Zai ci gaba da aiki yana chan, abinda doka ta ce a nan shine, idan shugaban zai bar kasa ne ya kai makonni uku baya nan, to amma a nan babu wannan maganar”
Garba Shehu ya kara da cewa Shugaban Kasar yana cikin koshin lafiya inda ya ce abin da ya kai shi kawai shine ya je duba lafiyar shi.
“Magana ce ta duba lafiya, ba wai ko wata jinya ce ta gaggawa ke damun shi ba, babu wani ciwo tattare da shi a yanzu haka”