Ma’aikatan gwamnati a jihar Kano da ke na zargin gwamnatin da biyansu albashin watan Disambar bara kan tsohon tsarin mafi ƙarancin albashi na dubu goma sha takwas.
Wannan na zuwa ne kasa da makonni uku da kungiyar ƙwadago, NLC a jihar, inda ta gargadi gwamnatin ta Kano da kar ta kuma datse wa ma’aikatan albashinsu na watan Disambar 2020, inda har ta yi barazanar tafiya yajin aiki idan aka sake taɓa musu albashi.
To sai dai gwamantin jihar Kanon ta ce yanke albashin ma’aikatan ya biyo bayan yadda cutar korona ta shafi kudaden da jihar ke samu ne, tare da tattalin arzikin Najeriya, shi ya sa ba za ta iya biyan ma’aikatan kan mafi karancin albashin na naira 30,000 ba.