Daga Muhammad Gambo Damaturu.
Gwamnatin Jihar Yobe ta yi bayani a kan dalilan da suka sa, ta rage albashin ma’aikatan kananan hukumomin ta a watan Yuli, inda ta ce hakan ya faru ne sakamakon koma bayan tattalin arzikin da kasa Nigeria ke ciki.
Kwamishinan Yada Labarai da Al’adun Gargajiya na jihar, Alhaji Abdullahi Bego ne ya bayyana haka, a wani taron da yi da l manema labarai daya gudana a Sakatariyar Kungiyar ‘Yan Jaridu reshen Jihar ta Yobe, dake birnin Damaturu a jiya ranar Alhamis, 5 ga watan Agusta 2021.
Bego yace, ya yi farin cikin kasance wa da manema labarai a wannan lokaci, domin tattauna muhimmin al’amari wanda ya jawo maganganu daban-daban a yan kwanakin da suka gabata, daga dai-dai-kun mutune da kungiyoyi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Harkar Film Bai dai na yi da ni ba, inji Baba Ari
“Kamar yadda mafi yawa daga cikin ku anan kuka sani, Gwamnatin Jihar Yobe ta na bada kulawa ta musamman wajen biyan albashin ma’aikata, a lokacin da ya dace, hakan ya sa albashi yake zama na farko cikin abun da ake soma cirewa daga kudin ta na shiga a koda yaushe”.
“Wannan ne yasa a kowane karshen wata Gwamnatin ta ke soma biyan albashin ma’aikata kafin ta yi la’akari da duk wani aiki”, inji Abdullahi Bego.
Kwamishinan ya ce, wannan abu ne dake a zahiri tsawon shekaru, inda Gwamnatin Jihar ta kara tabbatar da cewa, dukkan ma’aikaci yaji kararrawar shigan albashin sa da zarar lokaci ya yi.
A cewar Kwamishinan, a wannan lokaci kuwa, koma bayan tattalin arzikin da duniya ta shiga, wanda ya auku sakamakon barkewar cutar Korona, Gwamnatoci da dama sun shiga mawuyacin yanayi, Wanda hakan ne ya tilasta musu neman mafita.
Ya ce, ganin cewa hakki ne da ya rataya a wuyan Gwamnati, ta kula da lafiya, ilimi da walwalar al’umar ta, dole ne ta bi duk hanyar da tafi dacewa, don cimma nasara.
“Da farko, ta dauki matakin rage kudaden da take bai wa ma’aikatu, don gudanar da ayyukan yau da kullum, hakan bai Isa ba, ta sake rage kashe kudade a wuraren da basu dace ba, tare da sauya akalar kudaden, zuwa inda yafi dace wa da sauran su”.
“Bayan haka daukan wadannan matakai, har yanzu lamura na kara kamari, sai Gwmnatin ta ziyarci makobtan jihohi, don duba yadda abubuwa ke tafiya, anan ne ta samu hanyoyi biyu, na farko rage ma’aikata, na biyu kuma rage albashi, inda ta zabi rage albashin a maimakon korar su”, inji Abdullahi Bego.
Daga Karshe dai Kwamishinan ya ce, rage albashin ba na din din din bane, don kuwa da zarar al’amura sun dawo yadda suke a baya, zata maida musu albashin su yadda yake a can baya.
Ya kuma bayyana cewa kafin Gwmnatin Jihar Yobe, ta dauki wannan mataki, sai da ta nada Kwamiti wanda ya zauna, da shuwagabannin kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomin (NULGE), Kuma aka cimma matsaya guda, da kuma aka yada takardun nuna za’a aiwatar da haka.
Taron dai ya kunshi Kwamishinan Ma’aikatar Kula da Kananan Hukumomi da Masarautun Gargajiya, Alhaji Yerima Lawan Mahmud, da sauran manyan Jami’an Ma’aikatar jihar.
Comments 1