A dai dai lokacin da ake shirin gudanar da zaben fidda gwani cikin yan takarkarun Mukaman siyasa daban daban, da nufin karawa a babban zaben 2023 dake tafe, yanzu haka naɗaɗɗu a Mukaman siyasar na ci gaba da ajiye Mukaman su.
Yawan cin Kwamishinoni a jihohi 36 na kasar nan, na ci gaba da ajiye Mukaman su da nufin tsayawa takarar kamar yadda Dokar zaben da aka yiwa kwaskwarima ta bukaci hakan.
A jihar Kano baki daya wadanda suke son tsayawa takara tuni suka ajiye Mukaman su, yayin da wasu daga cikin gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya ki amincewa da ajiye nasu muƙamin.
A jihar Sokoto kuwa, a ƙalla Kwamishinoni 13 ne suka ajiye shahadar su domin tsayawa takarar a zaben 2023, bayan da gwamnatin jihar ta bukaci su aiwatar da hakan.
Yanzu haka dai rahotanni da jaridar Dimokuraɗiyya ta samu sun bayyana cewa akwai Kwamishinoni sama da 60 da suka ajiye Mukaman su a jihohi Najeriya 36.
Jihar Kano tana da kusan 10, Sokoto tana da 13, Delta kuwa akwai 9, haka lamarin yake a jihar Kwara inda 7 yanzu haka suka hakura da Mukaman nasu, yayin da jihar Bayelsa 5 suka ajiye nasu muƙamin.
To a matakin gwamnatin tarayya a iya cewa lamarin ya sha banban, domin kuwa jam’iyyar APC ta baiwa Ministoci da sauran masu son tsayawa takarar awanni 72 domin suyi murabus.
Chukwuemeka Nwajiuba karamin ministan Ilimi ne a Najeriya, ya bugi kirji tare da cewa ba zai sauka daga mukamin sa ba sai ya rage kwana 30 kafin babban zabe.
Ya kafa hujja da kundin tsarin mulki kasa, tare da watsi da sabuwar dokar zabe da abinda tayi tanadi.
Ya kuma bukaci duk wanda yake ganin ya saba masa kan wannan mataki na sa da ya zarce kotu domin kalubalantarsa a can.
Wannan dai na zuwa ne dai dai lokacin da kungiyar ASUU ke Yajin aiki, lamarin da yan kasar ke ganin ta kamata ya mayar da hankali wajen warware matsalar su maimakon tsayawa takara.
Yanzu dai akwai ministocin Buhari da dama da ke son tsayawa takara, amma har kawo yanzu shiru kake ji kan batun su ajiye Mukaman su.