Rahoton DSS ya yi Gargaɗi kan Zanga-zanga — Ngige ya shaida wa NLC
Gwamnatin Tarayya ta roki Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya da ta soke zanga-zangar da ta ke shirin yi dangane da tsawaita yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’o’iami’o’i da sauran Ƙungiyoyin jami’o’i.
Ministan Ƙwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige ne ya yi wannan roƙo a ranar Alhamis a wani taro da shugabannin kungiyar NLC a ofishin sa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Badaƙalar Biliyan 109: EFCC zata gurfanar da tsohon AGF, Idris, a yau Juma’a
Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Ƙaramin Ministan Ƙwadago da samar da ayyukan yi, Festus Keyamo; da Babbar Sakatariya ta Ma’aikatar, Madam Kachollom Daju.
Ngige, a nasa jawabin, ya yi ƙarin haske ga shugabannin ƙwadago a ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ta ke yi kawo yanzu na warware matsalar da ta addabi ɓangaren jami’o’i.
A ranar 17 ga watan Yuli ne ƙungiyar NLC ta sanar da cewa za ta gudanar da zanga-zanga a fadin kasar a ranakun 26 da 27 ga watan Yuli domin matsa wa Gwamnatin Tarayya lamba kan ta warware yajin aikin da ASUU da sauran kungiyoyin jami’o’i suka yi na tsawon watanni biyar.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa ASUU ta fara yajin aiki a ranar 14 ga watan Fabrairu, bisa abin da Kungiyar ta bayyana a matsayin gazawar gwamnati wajen magance wasu bukatun ta.
A wata sanarwar Manema Labarai ɗauke da sa hannun Jami’in Hulɗahulda da jama’a na Ma’aikatar Ƙwadago da samar da ayyukan yi ta tarayya, Olajide Oshundun, ministan ya tunatar da shugabannin kungiyar ta NLC cewa ya shigar da su cikin sulhun bangarorin uku da ke gudana a ma’aikatar sa, da kuma sanin ƙoƙarin gwamnati don warware matsalar, ba za su iya yin wani gangami ko zanga-zanga ba.
Ya kuma shaida wa Shugabannin kwadago cewa Majalisar zartaswa ta Tarayya ta umarce shi da ya sanar da su irin mumunan illar da suka shafi tsaro a zanga-zangar da aka shirya yi.
A cewarsa, wani rahoton tsaro da Ma’aikatar Harkokin wajen kasar ta aike wa ofishinsa, ya yi Gargaɗi da kakkausar murya kan gudanar da zanga-zangar.
Ya bukaci kungiyar NLC da ta sake duba taron da aka shirya domin ɓata gari na iya yin amfani da shi wajen kawo taɓarɓarewar tsaro.
Ngige ya bayyana damuwar Gwamnati cewa ƴan siyasa za su iya ba da kudi a taron da za a yi a barna a kasar nan.
Ya ci gaba da cewa, “Talakawa na iya yin kuskuren fassara taron a matsayin wata dabarar da kungiyar NLC ke yi na kara ƙaimi ga ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, lamarin da zai iya tunzura magoya bayan sauran jam’iyyun siyasa cikin tashin hankali.
“Sashe na 40 na kundin tsarin mulkin kasar ya fito karara kan ‘Yancin kungiyoyi. Daya daga cikin tanade-tanaden shi ne, mutane masu irin wannan tunani za su iya tsara kansu su kafa jam’iyyar siyasa.