Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu a ranar Talata ya ce gwamnatinsa ta dukufa wajen tabbatar da adalci da gaskiya dangane da rahoton kwamitin #EndSARS na jihar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kwamitin ya gabatar da rahotonsa ne a ranar 15 ga watan Nuwamba, duk da cewa har yanzu gwamnatin jihar ba ta bayyana abun da ya kunsa ba.
Sai dai wani bayanin da aka bankado ya tuhumi sojojin Najeriya da gwamnatin jihar Legas da kashe masu zanga-zangar da ba su dauke da makami a kofar Lekki Toll. Har yanzu dai ba a bayyana yadda aka fitar da rahoton ba.
Sanwo-Olu, da yake tsokaci kan rahoton, ya ce fallasa abun “abun takaici ne. Yayin da nake yaba wa kwamitin da ya gudanar da aikinsa gwargwadon iyawarsa, amma abun takaici ne yadda aikin kwamitin da fitar da rahoton ba da izini ba ya haifar da tashin hankali. Abun bakin ciki, an sake bude wani rauni mai zurfi,” in ji shi.
“Wasu zafafan kalamai da aka yi a tsakanin ra’ayoyi daban-daban kan rahoton, abun takaici ya sanya mu duka cikin hadarin rasa babban hoto; kasancewar abin da muke nema a bainar jama’a ita ce wadda dukkanmu muna cikin koshin lafiya, an amince da jami’an tsaro, kuma an tabbatar da adalci ga kowa.
“Kamar yadda na bayyana a baya, ba mu da niyyar tsunduma cikin ayyukan tarihi ko kara ruru wutar sha’awa a kan al’amarin da ya haifar da sha’awa da cece-kuce a cikin kasa da ma duniya baki daya.
“Hukunce-hukuncenmu da ayyukanmu za su dogara ne kacokan bisa doka, ingancin shaida, da kuma mutunta gaskiya marar lahani,”acewarsa