Shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai ya bayyana cewa kididdigar da kungiyar ‘Transparency International’ ta yi a Najeriya ya kara tabbatar da matsayar da suka yi a baya cewa jam’iyyar APC mai mulki tana da matsala akan cin hanci.
Matsayin Najeriya na 154 a halin yanzu a cikin kasashe 180 a cikin 2021 masu hasashen cin hanci da rashawa ya ragu da 149 a cikin 2020.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Ndudi Elumelu, ya ce ya ji takaicin yadda Najeriya ta kasance kasa ta biyu a Afirka ta Yamma da cin hanci da rashawa da kuma kasashe 154 cikin 180 a duniya.
Elumelu ya zargi gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC da rashin tunani da shirye-shirye da za su yi tasiri ga ‘yan Najeriya.
Sanarwar ta kara da cewa, “shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai ya damu matuka kan rahoton kungiyar Transparency International (TI) na shekarar 2021, wadda ta bayyana Najeriya a matsayin kasa ta biyu mafi cin hanci da rashawa a yammacin Afirka da kuma kasashe 154 daga cikin 180 a duniya.
“Rahoton TI ya tabbatar da matsayin su kai tsaye cewa jam’iyyar (APC) da gwamnatinta ba su da fata da cin hanci da rashawa da rashin tunani da shirye-shirye da ba za su yi tasiri ga jama’armu ba.
“Rahoton TI ya kuma tabbatar da matsayar marasa rinjaye na cewa jam’iyyar APC mafaka ce ta cin hanci da rashawa, wanda ke bayar da fakewa ga ‘ya’yanta masu cin hanci da rashawa su cigaba da wawure dukiyar kasa; cigaban da ya kawo tabarbarewar ababen more rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki a kasar.
“Bugu da kari kuma, marasa rinjaye ya yi la’akari da yadda Najeriya ke cigaba da samun koma-baya na cin hanci da rashawa tun bayan da jam’iyyar APC ta karbi mulki a shekarar 2015. Wannan ya nuna cewa al’amura da matsalolin da ke addabar ‘yan Nijeriya za su cigaba da tabarbarewa muddin APC ta cigaba da mulki.
“Irin wannan cin hanci da rashawa yana da alaƙa da alkawuran karya da da’awar aikin ƙarya, waɗanda suka kasance hannun jarin APC da gwamnatinta.
“A matsayinmu na wakilan jama’a, marasari jayen sun kara tsaurara hanyoyin bincike musamman wajen sanya ido sosai kan duk wasu tanade-tanade da ke cikin kasafin kudin 2022 don tabbatar da isar da duk wasu abubuwan da aka amince da su.
“Bugu da ƙari kuma, ƙungiyar marasa rinjaye tana ba da tabbacin cewa ba za ta taɓa yin kasa a gwiwa ba wajen fafutuka don kyautata rayuwar jama’a, kuma tana kira ga ‘yan Nijeriya da su mai da hankali kan aniyarsu ta fitar da jam’iyyar APC a 2023 tare da samar da gwamnatin da ta kula da muradunsu da gaske.”