Gwamnatin jihar Zamfara a yau Litinin za ta fara raba kayan abinci domin watan Ramadan ga marayu dubu hudu a tsakanin masarautu goma sha bakawai da ake da su a fadin jihar, daga kuma kananan hukumomi sha hudu da ake da su a dukkanin jihar. Da yake karin haske a garin Gusau, Sakataren gudanarwa na hukumar zakka da wakafi, Malam Bashir Sirajo, ya ce; an zabi marayu 1, 800 daga masarutu 16, yayin da aka yi marayu 3, 600 daga karkashin masarautar Gusau. Sirajo ya ce kowanne maraya za a bashi kayan abinci da ya hada da Suga, Shinkafa, wake, da kuma kayan sakawa tare da kudin da za su dinka kayan. Ya ce; za a kuma baiwa Masarauta naira miliyan daya da dubu dari takwas da kuma mota biyu da rabi dauke da abinci da kayan sakawa ga marayu dubu daya da dari takwas wanda masarautar ta tantance. A na shi bayanin, gwamnan jihar, Alhaji Abdulaziz Yari, ya garagdi wadanda aka damkawa ragamar raba abinci da ka da su ci amana, su kuma ji tsoron Allah. Ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi amfani da wannan wata na Ramadan wajen neman taimakon Allah da ya kawo zaman lafiya a jihar baki daya. Sannan ya gargadi ‘yan bindigar jihar da sauran masu tada zaune tsaye a jihar, da su tuba ko kuma su fuskancin sakamakon ayyukan da suke aikatawa. Rahotanni sun nuna cewa; an kaddamar da rabon raba kayan abinci ne da marayu 126 daga Gusau, inda su kuma Masarautar Gusau za ta raba sauran kayayyyakin, yayin da sauran kwamitin da aka nada za su raba sauran kayayyakin a sauran masarautun.