By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta fara gudanar da bincike kan zargin cin zarafi da wani magidanci mai suna Taofeek Gbolagade ya yi wa matarsa mai dauke da juna biyu.
An ce mutumin ya afka wa matarsa ne da duka bakakkautawa a gidansu da ke Ogbere, Ibadan, da sanyin safiyar Talata.
An tattaro cewa Gbolagade ya yi wa matarsa mai juna biyu dukan tsiya a kan Sahur, abincin da al’ummar Musulmi ke sha a shirye-shiryen azumin watan Ramadan.
Rahotanni sun bayyana cewa matar ta gaza shirya abincin sahur a kan lokaci sakamakon juna biyun da take dauke da shi inda ya lakada mata duka, sai dai wasu sun ce ba wannan ne ya sa mutumin ya yi wa matarsa dukan tsiya ba.
Rahotanni sun ce mutumin ya lakada wa matar duka sama da mintuna 30 kafin ta yi nasarar tserewa ta bar masa gidan.
An ce ‘yan uwanta ne suka kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda, yayin da kuma aka ce mijin ya gudu gida.
Wani makwabcin sa ya ce mutumin yana sha’awar dukan matarsa saboda wata ‘yar rashin fahimta data afku a tsakanin su.
Makwabcin ya ce, “Mijin bai damu da cewa matar tana da ciki ba. An rawaito ya yi mata dukan kusan minti 30 tana kuka, Daga karshe ta tsere ta gudu zuwa gidan iyayenta.”
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Adewale Osifeso, da aka tuntube shi, ya ce an fara bincike kan lamarin.
Comments 1