Kocin Ƙungiyar kwallon kafa ta PSG dake Ƙasar Faransa Mauricio Pochetino ya fito ya yi magana kan rade-radin da ake yi cewa Ƙungiyar na shirin yin wuff da Mai tsaron bayan Real Madrid kuma kyaftin dinta Sergio Ramos.
Kocin ya ce lallai Ƙungiyar tana kokarin inganta ko wane ɓangare a cikin fili, to amma dai bai bayyana matsayar batun na kafafen yaɗa labarai ba.
A yanzu haka ana ta yawo da maganar Ramos Kororo-kororo kan makomarsa a Real, ganin cewa kwantiraginsa da kungiyar zai kare a watan Yunin gobe.
Har kawo yanzu Madrid ba ta cimma matsaya ba dangane da makomarsa a Ƙungiyar, kuma PSG na kan gaba daga cikin kungiyoyi dake zawarcinsa.