Sufeto Janar na ‘yan Sandan Nijeriya, IGP Mohammed Adamu ya bai wa jami’an tsaron ‘yan sanda umurnin tsaurara tsaro a ofishin jakadodi da kuma wuraren huldar diflomasiyya da wuraren kasuwancin ‘yan kasar waje dake cikin Nijeriya.
IGP Mohammed Adamu ya ba da wannan umurnin ne a wata sanarwa da Kakakin ‘yan Sandan, DCP Frank Mba ya fitar a ranar Laraba a Legas. IGP Mohammed Adamu ya ce wannan umurnin ya zama dole duba da yadda wadansu suka fara kai harin ramuwar gayya ga wuraren kasuwanci na Shoprite dake Lekki a Legas a ranar 3 ga watan Satumba bisa zargin kashe ‘yan Nijeriya a Afrika ta Kudu.
Sufeto Janar din ya ce wadansu bata gari sun sace wadansu kayayyakin wuraren kasuwancin a yayin zanga-zangar da suka fito bisa kashe-kashen da ake yi a Afrika ta Kudu. Ya ce; da wannan yake umurtar dukkanin jami’an ‘yan sanda da su zama cikin shirin ko ta kwana wajen ganin sun dakile bazaranar haifar da tashin-tashina irin wanda ke aukuwa a Afrika ta Kudu a fadin Nijeriya.