Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce rayuwar kowanne dan Nijeriya a duk inda yake a fadin duniyarnan, yana da daraja, inda ya yi alkawarin bunkasa alakar gwamnatinsa domin ganin ya kare dukkanin rayukan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da nisan da ke tsakanin Nijeriya da inda suke rayuwa ba.
Kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, shi ne ya tabbatar da hakan a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a a Abuja, inda ya ce shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a yayin da ya gana da ‘yan Nijeriya mazauna kasar Rasha.
Shugaba Buhari ya ce; “Gwamnatinmu za ta kare dukkanin ‘yan Nijeriya a gida da kuma kasashen waje.” In ji shugaba Buhari, a yayin da yake ganawa da dalibai, da kuma masana a birnin Sochi na kasar Rasha, a yayin da yake gab da kammala halartar taron kwana uku na bunkasa Alakar kasar Rasha da Afrika, wanda ya samu halarta.
Akalla shugabannin kasashen Afrika 40 ne suka samu halartar taron.