Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin a sake bude makarantun kasar don bai wa daliban makarantar Sakandare da ke a ajin karshe damar rubuta jarabawarsu ta WAEC, a yayin da kasar ke ci gaba da yakar annobar korona.
Daga ranar 5 ga watan Augusta mai kamawa daliban za su koma makaranta a yayin da ake sa ran su rubuta jarabawar, a ranar sha bakwai ga watan goben.
A baya can an yi zatan daliban ba za su sami damar zana jarabawar ba, bayan da gwamnati ta baiyana damuwarta a saboda karuwar yaduwar cutar Coronavirus a kasar.