An samu rabuwar kawuna tsakanin jihohin Nigeria, tun bayan da gwamnatin tarayya ta sanar da matsayarta na duba yiyuwar canja ranar bude makarantun kasar, biyo bayan karuwar sabbin mutanen da ke kamuwa da cutar COVID-19 a kasar.
Canja ranar bude makarantun da gwamnatin kasar ke shirin yi ya jawo sabanin fahimta a tsakanin jihohin, wadanda tuni suka sanar da ranakun da za su bude makarantu a jihohin su.
Ya zuwa yanzu babu wani taka mai mai lokacin bude makarantun gwamnati na Nigeria, kamar yadda binciken jaridar The Nation ya nuna.
Gwamnatin tarayya ta ce ba wai ta dage ranar bude makarantun bane har sai baba-ta-gani ba. Don haka, makarantu da yawa na shirin bude makarantu a ranar 18 ga watan Janairu kamar yadda kwamitin PTF na COVID-19 ya bayar da umurni.
KARANTA WANNAN: ‘Yan Sanda Sun Kama Mutum 12 Da Ake Zarginsu Da Fashi Da Makami A Kano
A ranar Litinin, ministan ilimi, Mallam Adamu Adamu, yayin amsa tambayoyi daga manema labarai ya bayyana cewa gwamnati na duba yiyuwar canja ranar bude makarantu daga 18 ga watan Janairu zuwa wata rana ta daban.
Mai magana da yawun ma’aikatar lafiya ta kasa, Ben Goong, ya shaidawa wakilin The Nation cewa mutane ne ba su fahimci abinda shi ministan ya ke nufi ba.
“Idan misali a yau ko gobe, kwamitin PTF ya ce: ‘Bisa la’akari da rahotannin da muke samu, kowa ya zauna a gida,’ to, dole ne a canja ranar bude makarantu.”
Wasu jihohi sun amince makarantu su fara aiki a ranar 4 ga watan Janairu. Kadan daga makarantun ne suka bude a ranar Litinin, yayin da wasu ke jiran ranar 18 ga watan Janairu domin bude makarantun su.